-Yakin neman kujerar gwamnan jihar Edo ya ta’allaka ne tsakanin Pasto Osagie Ize-Iyamu na PDP da Godwin Obaseki na APC – Basaraken Uromi, wani gari a cikin jihar ya bayyana abin da ya faru tsakaninsa da Ize-Iyamu lokacin da ya kawo masa ziyara -Ya gaya ma Obaseki cewa bai amince da Ize-Iyamu ko PDP ba […]
The post PDP ta bamu N6 miliyan domin goyon bayan Ize appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
-Yakin neman kujerar gwamnan jihar Edo ya ta’allaka ne tsakanin Pasto Osagie Ize-Iyamu na PDP da Godwin Obaseki na APC
– Basaraken Uromi, wani gari a cikin jihar ya bayyana abin da ya faru tsakaninsa da Ize-Iyamu lokacin da ya kawo masa ziyara
-Ya gaya ma Obaseki cewa bai amince da Ize-Iyamu ko PDP ba saboda rashin cika alkawurran da suka yi ma kasar Esan
Osagie Ize-Iyamu
Wani babban basarake a jihar Edo ya fallasa yadda Pasto Osagie Ize-Iyamu, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben da za’a yi tare da Chief Tony Anenih, suka bashi tare da wasu sarakunan cin hancin N6.00 miliyan domin neman goyon baya.
Tony Anenih, dan kasar Uromi ne kuma tsohon shugaban kwamitin amintattu na PDP, amma basaraken yace bai amince masa ba ko Ize-Iyamu Mai martaba, Anslem Okojie, Onojie na Uromi ya bayyana ma Godwin Obaseki, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, wanda ya kira abokinsa,
Basaraken ya ba Obaseki goyan bayansa lokacin da shi Obaseki ya rasa magoya baya fiye da 700 a karamar hukumar Ovia ta arewa maso gabas ta jihar
KU KARANTA : Wani shugaban jam’iyar APC Femi Adeyemi ya rasu
Ga abin da yace game da Ize-Iyamu: “lokacin da yazo fadata, mu 29 ne, kuma ya bamu N3.00 miliyan . Muna da abinda muke kira kokas a kasar Esan, kuma nine shugaba. An ba mambobin kokas N500,000. Yayin da PDP tace zata kaddamar da yakin zabe a Uromi, Onojie na Ewu ya Kira ni yace PDP zata bada N3.00 miliyan amma yana ganin sunyi kadan. Yace mu Gaya ma pasto ya maida kudin N10.00 miliyan goma ko kuma mu gaya ma gwamnan gurguzu ya bamu N10.00 miliyan. Daga karshe da suka zo, Anenih ya kawo N3.00 miliyan, Ize-Iyamu ya kawo N3.00 miliyan. N6.00 miliyan aka kawo mani a fadata”
The post PDP ta bamu N6 miliyan domin goyon bayan Ize appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.