Wani mutum mai suna Peter Ayewoh ya mutu a ranar laraba 3 ga watan agusta yayin wani zanga zangar lumana da kungiyar ma’aikatan kanananan hukumomi reshen jihar Edo ta gudanar. An ruwaito cewa mamacin ya rasu ne bayan faduwa da yayi a lokacin da ake gudanar da zanga zangar. Jaridar Nigeria Tribune ta ruwaito cewa […]
The post Ya mutu yayin zanga zanga rashin biyan albashi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Wani mutum mai suna Peter Ayewoh ya mutu a ranar laraba 3 ga watan agusta yayin wani zanga zangar lumana da kungiyar ma’aikatan kanananan hukumomi reshen jihar Edo ta gudanar.
An ruwaito cewa mamacin ya rasu ne bayan faduwa da yayi a lokacin da ake gudanar da zanga zangar. Jaridar Nigeria Tribune ta ruwaito cewa kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi wato NULGE ta shirya zanga zangar ne don nuna bacin ransu ga rashin biyan albashinsu na watanni 2 zuwa watanni 18.
Rahotanni sun nuna cewa masu zanga zangar sun tsayar da al’amura cak a wasu sassan jihar ta Edo. An wuce da gawar mamacin zuwa kauyen su Uromi dake babban birnin jihar Edo, Bini.
Kazalika yan sanda sun kai ma wasu ma’aikatan lafiya na asibitin koyarwa na jami’ar Jos a yayin da suke gudanar da zanga zangar lumana, inda hakan yayi sanadiyyar jikkata mutane 5 a ranar talata 21 ga watan yulio. Rahotanni sun nuna cewa yansanda sun harba barkono tsohuwa ne a tsakanin masu zanga zangar a lokacin da suka ki matsawa daga hanyar shiga asibitin.
The post Ya mutu yayin zanga zanga rashin biyan albashi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.