Wata ta sayar da dan cikinta kafin ta haife shi
-Wata mata furta cewa ta sayar dan da ke cinkinta tun kafin ta haife shi
-Matar ta kuma amsa zargin satar wasu yara a yankin
Wata mata ‘yar shekara 29 mai suna Chidinma Okorie furta cewa ta sayar da jaririn da ta ke dauke da shi a cikinta a kan Naira 100,000. Chidinma ‘yar asalin Amasiri a jihar Ebonyi, a ranar Alhamis ta ba jama’a mamaki a lokacin da ta furta cewa ta sayar da wasu yara uku a Umuoji ta karamar hukumar Idemili ta arewa a jihar Anambra tare da da hadin bakin wasu likitocin asibiti mai zaman kansa su biyu a yankin.
KU KARANTA:Yan sanda sun bankado gidan sayar da jarirai a Enugu
Chidinma wacce ba ta aure ba, ta kuma haifi ‘ya ‘ya biyar a titi, a cewarta, wata mai wa’azin Krista ce ta shigar da ita wannan sana’a ta kuma kara da cewa, “… Na sayar da wasu yara su biyu a kan Naira 50,000 kowannen su, yanzu ina da ciki kuma madam mai wa’azi ta ce idan na haihu za ta sayi wannan jaririn a kan kudi Naira 100,000…”
Matar ta kuma kara da cewa, wacce suke sana’ar sayar da jariran da ita, ita ta kawo su daga Ebonyi zuwa Anambra, a inda kuma ta kai su wurin wani matsafi a Asaba, wanda ya sa suka yi ratsuwar sirri da jinni saboda kar so tona asirin juna.
Jami’ar ‘yan sanda, Misisi Nkieru Nwode ta rundunar ‘yan sandan jihar ce, ta bayyana cewa an kame wacce ake zargi ne tare da was, bayan da ‘yan sanda suka samu labari a ranar Laraba, Kakakin rundunar ta kara da cewa, satar da Chidinma ta yi na baya-bayan, nan shi ne na sace dan wani Fasto a yankin.
The post Wata ta sayar da dan cikinta kafin ta haife shi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.