Добавить новость


World News in Dutch


Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

Wayyo! A bayyana kudurorin Keshi kafin mutuwar sa 

Tsohon mataimakin mai horarwa Stephen Keshi Valere Hounandinou ya bayyana kudurorin da mamacin Keshi yake da su kafin mutuwar sa.

Shi dai mamacin wanda kuma shine tsohon jagoran kungiyar Super Eagles Stephen Keshi ya mutu ne a ranar 8 ga watan Juni bayan wata yar gajeruwar rashin lafiya.

Kafin mutuwar sa dai shine ya jagoranci kungiyar kwallon kafar Najeriya watau Super Eagles ya zuwa lashe gasar cin kofin kasashen Afrika wanda akayi a kasar Afrika ta kudu wanda hakan ne ma ya maida da mutum daya tilo da ya taba lashe gasar a matsayin dan wasa da kuma mai horarwa.

An dai rufe Keshi din a kauyen sa dake Ukpologwu Illah a jihar Delta.

A wata kebantacciyar fira da tsohon mataimakin nasa yayi da gidan jaridar NAIJ.com sashen wasanni, Hounandinou ya bayyana cewa aminantakar shi da mamacin ta soma ne tun a shekara ta 1979 a lokacin da suka buga wata gasa a kungiyar su ta ACB FC a garin Legas.

Da yake bayyana kudurorin mamacin kuma, Hounandinou ya ce Keshi din yana da kudurin wallafa littafi kan rayuwar sa da kuma fadi-tashin sa a bangaren wasanni dama horarwa sannan kuma har ilayau yace mamacin yana da kudurin bude makarantar koyon kwallon kafa irin na kasashen turai.

The post Wayyo! A bayyana kudurorin Keshi kafin mutuwar sa  appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media










Топ новостей на этот час

Rss.plus