–Fani-Kayode ya musanta taba cewa PDP ta nemi gafaran Shugaba Buhari. –Ya dau alwashin ba zai taba hada kai da su wajen cigaban Najeriya ba. Tsohon Ministan jirgin saman, Chif Olufemi Olukayode, wanda ya samu yanci kwanan nan daga garkama akan laifin babakere da kudin gwamnati, ya fara maganganu akan shugaba Muhammadu Buhari. Diraktan yada […]
The post Bayan kwashe makonni a tsare;Fani-Kayode bai daddara ba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
–Fani-Kayode ya musanta taba cewa PDP ta nemi gafaran Shugaba Buhari.
–Ya dau alwashin ba zai taba hada kai da su wajen cigaban Najeriya ba.
Tsohon Ministan jirgin saman, Chif Olufemi Olukayode, wanda ya samu yanci kwanan nan daga garkama akan laifin babakere da kudin gwamnati, ya fara maganganu akan shugaba Muhammadu Buhari.
Diraktan yada labarai na yakin neman zaben PDP, ya kasance a garkame bayan dakme shi da akayi a ranar 9 ga watan mayu,a Abuja. Daga baya aka tura shi Jihar Legas inda Hukumar hana Almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagwon kasa watau EFCC ta tuhume shi da laifuffuka 17, Amma bayan makonni a garkame, an ba Fani Kayode belin N250 miliyan a ranar 4 ga watan Yuli.
Tsohon Ministan wanda ya shahara da karfin hali da zakin baki, ya cigaba da maganganu aka shugaban kasa bayan ya musanta maganan da wani yayi masa a shafin sada zumunta ta Facebook.
KU KARANTA : An samu matar Obanikoro da cin hanci da rashawa- EFCC
Yayinda ya ke bada amsa ta shafin sa ta Facebook, Fani Kayode yace : “Akwai wani mara lafiya a Facebook wanda manna wani shirme yace ji na fada. Ya fadi cewa nace : Ina tunanin abinda ya kamata muyi,mu yan PDP shine mu nemi gafaran Shugaba Buhari da jam’iyyar APC, sannan mu hada kai kasu mu kawo cigaban Najeriya – femi fani- kayode.
“Ku sani cewa wannan karya, babu gaskiya a ciki. Ban taba fadin wannan abun ba a boye ko a bayyane, kuma ban taba wallafa shi ba a ko ina.Wannan kaidi ne iri iri da sukeyi domin taimaka ma kansu a wannan azzalumar gwamnati. Ina sake jaddada adawa ta ga gwamnatin Shugaba Buhari da jam’iyyar APC, kuma bazan taba ba wani shawaran ya hada kai da su.”
The post Bayan kwashe makonni a tsare;Fani-Kayode bai daddara ba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.