–Yan bindiga sunyi garkuwa da Oba Oseni a fadarsa a Jihar Legas –An harbi uwargidan sa kuma an kashe mai gadin sa. An samu wani tashin hankali a unguwar Iba a Jihar Legas bayan wasu yan bindigan yankin Neja Delta sunyi garkuwa da Oba Yushau Goriola Oseni. Game da cewar Jaridar PM news, yan bindigan […]
The post Yan bindiga sunyi garkuwa da Sarkin Gargajiya a Legas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
–Yan bindiga sunyi garkuwa da Oba Oseni a fadarsa a Jihar Legas
–An harbi uwargidan sa kuma an kashe mai gadin sa.
An samu wani tashin hankali a unguwar Iba a Jihar Legas bayan wasu yan bindigan yankin Neja Delta sunyi garkuwa da Oba Yushau Goriola Oseni.
Game da cewar Jaridar PM news, yan bindigan sun kai harin ne a ranan asabar ,16 ga watan yuli misalin karfe 11:30 na dare. Yan bindigan sun samu shiga fadar Oniba of Ibaland ne ta hanyar rafi ,suka kashe msi gadin sa.
Majiya a fada ta bada rahoton cewa wani makwabci ya sha harbin bindiga tare da uwargidan sarkin gargajiyan. Bayan Yan bindigan sunyi Garkuwa da shi, sun sake bi ta rafi suka gudu. Har yanzu ba’a sani shin sun yi garkuwa da shi don karban fansa ne,ko kuma cigaban hare haren da ake kaiwa Jihar Legas ne.
Hare-haren yan bindigan ta kara kamari, ta tashi daga yankin neja delta zuwa wasu sassan Jihar Legas musamman wuraren da ke kusa da hanyoyin ruwa.harin da suka kai yayi sanadiyar rasa rayukan mutane 4. Dolapo Opeyemi Badmus ,wadda itace kakakin jami’an yan sanda na jihar legas ya bayyana a wata hira da gabatar da Jaridar Naij.com cewa Hare-haren yan bindiga ke kaiwa legas da gaske ne kuma ofishin yan sanda na iyakan kokarinsu wajen kawo karshen abun.
KU KARANTA : Yan daba sun sari dan Jarida a Legas
Ta ce: “Wasu yan tayar da kayar baya da ke kiran kansu da yan bindiga sun fito daga yankin hanyoyin ruea saboda kusancinsu da ita, suna aikata ta’asa iri iri akan mazauna wurin. Yan tada kayar bayan sun fito wani sashin jihar legas mai suns igolomu cikin dare. Ofishin yan sanda na ankare da unguwar tunda muka samu kara. Mutane 4 rasa rayukansu a jihar legas yayinda 2 aka rasa a jihar ogun. Ofishin yan sanda bata ji dadin hakan ba, saboda haka ,muna kira ga jama’a da cewa su kawo kara duk wani abun zargin da suka gani.”
The post Yan bindiga sunyi garkuwa da Sarkin Gargajiya a Legas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.