Niger Delta Avengers sun saka bam a gangan man Agip
-Niger Delta Avengers sun ce sun sa bam a Obi Obi Truck Line na Agip ENI
-An kai harin ne da karfe 3 na dare, 10 ga watan Yuni
– Kungiyar Niger Delta Avengers sun ce sun saka bam a Obi Obi Brass Truck Line na Agip ENI.
A cewar kungiyar ta hanyar sadarwa na twitter sun ce filin mai da aka dana bam shine babban filin danyen man fetur na Agip dake jihar Bayelsa.
Ka tuna cewa, kungiyar sun ki yarda su sassanta da gwamnatin tarayya na Najeriya, duk da gwamnatin tarayya ta janye dakaru daga yanki da ke da arzikin mai na Niger Delta.
kungiyar sun ce suna farin ciki da cewan matatun mai na kasashen sun daina siyan mai daga Najeriya.
kungiyar NDA ya sha alwashin rage gurin samar da mai na Najeriya zuwa sifili(0) sun kuma gargadi kamfanonin mai da cewan kadda su gyara gurin shigar da mai.
ka tuna cewa, hujojin sun nuna cewa Najeriya ya rasa kimanin $6.72m(kusan naira biliyan 1.3) saboda zafin shigarwan bam a gurin arzikin mai na yankin Niger Delta da mayakan, Niger Delta Avenger(NDA) suka yi.
dala miliyan $6.72 aka isar saboda kullum ana asarar gangan danyen mai 140,000 daga filayen sarrafa danyen mai na jihar Bayelsa daga kamfanin Nigeria Agip Oil Company(NAOC) da Aiteo Oil da farashin mai $48 ko wani ganga.
The post Niger Delta Avengers sun saka bam a gangan man Agip appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.