An yi Allah wadai da hari akan Francis Emmnuel Kaduna
Jaridar Punch ta ruwaito Bishof na garin Sokoto Rev. Mathew Kuka yana cewa yazama dole ne a kamo wadan da suka yi aika-aikar sannan kuma a hukunta su.
Bishof din kuma ya nuna damuwar sa a kan yadda tsatssauran ra’ayin addini ke sa mutane na aikata munanan aiyyuka kamar hakan. Wasu matasa ne dai suka kai ma Emanuel Francis hari saboda baya azumi.
KU KARANTA: An saka Bam a Obi Truckline
Shikuwa babban lauya na garin Legas Mr. Femi Falana ya bayyana cewar dole ne gwamnatin Najeriya ta gano hanyar da za’a magance wadan nan tashe tashen hankulan na addini da wuri sannan kuma a hukuta masu yi don ya zama darasi ga saura.
Shima dai shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna Mr. Sunny Oibe ya bayyana wadan da suka yi aika-aikar a matsayin marasa son zaman lafiya kuma makiya Najeriya. Tuni dai gwanman jihar kaduna din Nasir El-rufai ya yi tir da harin kuma har ya ziyarci Emmanuel din a asibiti sannan kuma ya ummurci yan sanda da su gano tare da kamo wadanda suka yi aika-aikar.
The post An yi Allah wadai da hari akan Francis Emmnuel Kaduna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.