– Shugaban majalisar Dattawan Najeriya da Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu sun dan kwana biyu fadan siyasa
– Akwai lamarun cewa sun daidai tsakanin su a jiya 31 ga watan Mayu
– Atiku, Oyegun ne suka daidaita tsakanin su
Naij.com ta samu hotunan taron da akayi tsakanin Shugaban majalisar Datawa, Sanat Bukola Saraki da tsohon Gwamna Jihar Legas Bola Ahmad Tinubu a jiya Litinin 30 ga watan Mayu na 2016 a babban birnin Najeriya Abuja.
KU KARANTA: Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin
Su biyun sun dan kwana biyu suna rigimar siyasa tun bayan da shugaban majalisar Dattwan ya samu mukamin shi bayan da jam’iyyar ta nemi daya janye daga neman kujerar a watan Mayu na 2015 daya wuce.
Wasu majiyoyi sun bayyyana cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar APC John Oyegun ne suka hada taron dan a shirya su.
Bola Ahmad Tinubu da Bukola Saraki sun sha alwashin zasu tsagaita wuta kuma suyi aiki hannu da hannu domin su tallafama jam’iyyar ta cinma matsayar ta.
Naij.com tayi kokarin ta tuntubi Mr Sunday Dare, jami’I mai taimaka ma Bola Tinubu akan hudda da jama’a bai don taji daga wurin shi bai dauki wayar da aka kira shi ba.
Tuni wasu na ganin cewa wannan zaya kawo karshen shari’ar Saraki a kotun CCT.
A wani labarin, Naira na cigaba da karewa inda a sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya ke shirin shigowa da wani sabon tsari domin Gwamnatin na shirin fidda hannun ta daga harkar canjin kudade.
Wannan ne ya sanya Dala daya a yau ta koma N285 a Bankuna. Wannan yazo ne bayan da gwamnati ta cire tallafin Man fetur, ta kuma kara kudin wutar lantarki.
Gwamnati ta sha alwashin tallafawa yan Najeriya Miliyan daya da Naira N5000 a kowanne wata. Wannan zaya rage radadin talauci sannan kuma ya basu damu su tallafawa iyalan su kuma su cigaba da gudanar da rayuwar su.
The post Atiku, Oyegun sun daidai tsakanin Tinubu da Saraki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.