Kamar yadda muka saba kawo maku manyan labarai daga jaridun Nijeriya a yau, Talata, 31 ga watan Mayu ma gamu da manyan Labarai daga wasu jaridu
Farkon, a Jaridar The Nation mun samu rahoto inda Gwanar jihar Imo mai suna Owelle Rochas Okorocha yace wanda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tana gina sabon Najeriya.
KU KARANTA KUMA:Wasu labarai acikin jaridun Nijeriya a yau, Juma’a
Inda a cikin Jaridar The Punch kuma mukaji Sanata Ben Murray-Bruce ya bayyana yadda hukumar DSS ta kange shi daga gaishe da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasar tarayyar Najeriya, Abuja.
Yayin da jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wanda Manjo Al-Mustapha yace wanda ya kusa bayyana yadda tsohon shugaban kasa akarkashin gwamnatin soji mai suna Janar Abacha da manyan dan Najeriya da kuma manyan dan siyasa mai suna Cif MKO Abiola suka mutu.
Jaridar Daily Independent ta bayyana cewa, Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya kalubalanta Gwamnatin Tarayya inda yake cewa, baka isa ka hana ni tafiya kasashen waje ba.
A karshe a jaridar The Sun munji cewa wanda wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai suna Cif Ebenezar Babatope yace, muna bikin shekara daya a cikin bakin ciki.
A wasu labaran duniya, wani Ministan ya sake yin murabus a Brazil. Wasu yan kasar Chadi sun fara tofa albarkacin bakinsu game da daurin rai da rai da wata kotu a Senegal ta yanke wa tsohon shugaban kasar Hessene Habre.
Yan majalisar dattawan Amurka daga jam’iyyar Republican na yin kafar-ungulu ga yunkurin shugaban Obama na rufe gidan kason Guantanamo
A kasar Ghana kuma ana ci gaba gano gwawwakin mutanen da hadarin kwale-kwale ya ritsa da su. A Najeriya, wasu jihohi za su kaddamar da wani tsarin noma da zai taimaka wajen habaka sana`ar ta yadda manoma za su kasance masu dogaro da kansu.
The post Labarai masu muhimmanci acikin jaridun Najeriya a Talata, 31 ga watan Mayu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.