Nijeriya ta shahara a rashawa: Buhari ya goyi bayan Firaym Minista Cameron
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wata hira da yayi da gidan talabijin na CNN ya nuna yardar shi da maganar da Firaym Minista David Cameron ya yi a kan Nigeria
– Ya bayyana cewa gwamnatinsa tafi damuwa da kawo karshen al’amarin ba yin maganar ta ba
Buhari a London
Shugaba Buhari ya gasgata kalaman Firaym Minista David Cameron na cewa Nijeriya ta shahara a fagen cin hanci da rashawa. Ya kuma kara da cewa yafi maida hankali akan yakin da yake da cin hancin da rashawa ba yin surutu na fatar baki a kan ta ba.
KU KARANTA WANNAN: Jiga jigan jam’iyyar PDP za su janye su shirya taron su daban
Ya bayyana cewa gwamnatin sa ta na wasu shirye shirye ne na korar dumbin ma’aikatan gogi da ke karbar albashi a yaudare da kuma kama wadanda sukayi almundahana da kudin jama’a a gwamnatin da ta gabata.
Ya fada ma CNN cewa wasu masu mukami a gwamnatin da ta gabata sun hadu kamar a taron cin abinci sun kasafta biliyoyin dollolin da aka ware domin kawo karshen matsalar ‘yan ta’addan Boko Haram.
The post Nijeriya ta shahara a rashawa: Buhari ya goyi bayan Firaym Minista Cameron appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).