– A yau za’a cigaba da Shari’ar Saraki
– Kotun CCT zata cigaba da shari’ar bayan da kotun Koli ta amince a cigaba
– Saraki ya musanta duka zargin da ake yi mashi
A yau ne kotun CCT dake Abuja zata cigaba da sauraron Shari’a akan zargin da hukumar CCB take yima shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, akan kin kayyaje dukiyoyin sa a lokacin da yake gwamnan Kwara.
Wannan na zuwa bayan da lauyan Saraki ya nemi a daga Shari’ar daga 10 ga watan Maris zuwa 11 ga watan Maris domin Saraki ya samu damar halartar wasu lamurra masu amfani.
KU KARANTA: Buhari ya canza ma’aikata 184
Cigaban shari’ar na zuwa ne bayan da shugaban Majalisar Dattawan ya nemi kotun daukaka kare dake Abuja da ta CCT umurni ta dakata da cigaban Shari’ar, amma kotun sai ta bayyana cewa kotun nada hurumin gurfanar dashi. Daga nan ne sai Saraki ya tafi kotun koli inda ya nemi a duba inganci Shari’ar da take yi mashi, inda itama ta jaddada ikon kotun na CCT.
Kotun na zargin shi ne da laifuka 13 wadanda duka ya musanta cewa shi baya da laifi inda yake zargin cewa abokan adawa ne daga wajen majalisa suka kunno mashi wannan matsalar.
KU KARANTA: Manyan labarai 10 na ranar Alhamis
Da farko yaki zuwa kotun bayan data kira shi, ko da kotun ta bashi ta nemi ta bada umurni a kama shi sai yazo kotun inda yazo tare da Yan uwan shi Santaoci sama da 60 a kotun.
The post Yau za’a cigaba da Shari’ar Saraki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.