Boko Haram ta bullo da wata hanya don kashe mutane
Kungiyar Boko Haram ta bullo da wata hanya domin ta kashe mutane. Wannan hanya itace kira ga mutane da suyi kofi din katin zabe su kai hukumar zabe don aba su Naira dubu shidda.
Yan ta’addan Boko Haram
Gwamnatin jihar Borno tayi gargadi ga al’umma inda tayi kira da ayi watsi da wannan zancan kuma mutane suyi a hankali don kada a rude su.
Cewa: “An jawo hankalin mu akan cewa kungiyar Boko Haram nayin kira ga al’umma da suyi kafi din katin zabe su kai hukumar zaben don abasu Naira Dubu shidda. Bincike ya nuna cewa yan Boko Haram ne suka kawo wanna labarin don su tara mutane su tada masu bam.
“Muna kira ga mutane su sani cewa idan gwamnati na son ta aika sako zuwa ga mutane, muna amfani ne da jaridu da kuma sauran sanannun kafen yanar gizo.”
The post Boko Haram ta bullo da wata hanya don kashe mutane appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.